Najeriya ta lallasa Kamaru da ci biyu da nema a gasar cin kofin Afirka

0
121

Daga Ibraheem El-Tafseer

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da ta doke Kamaru 2-0 a wasan zagaye na biyu a gasar kofin Afirka.

Tun kan a tafi hutun rabin lokaci, Super Eagles ta ci ƙwallon farko ta hannun Ademola Lookman, kafin nan an soke wadda Semi Ajayi ya fara cin Kamaru.

Bayan da suka yi hutu ne suka koma zagaye na biyu Kamaru ta yi ta ƙoƙarin farke ƙwallon da aka zura mata, amma ba ta samu dama da yawa ba.

Daf da za a tashi daga karawar ce Super Eagles ta ƙara na biyu ta hannun Ademola Lookman, hakan ya sa tawagarta kai zagayen quarter finals.

Da wannan sakamakon Najeriya za ta fafata a zagayen daf da na kusa da na ƙarshe da Angola ranar Juma’a 2 ga watan Fabrairu.

Gabanin fafatawar Najeriya da Kamarun a ranar Asabar, Angola ta doke Namibia 3-0 a wasan farko a zagaye na biyu a wasannin da ake buga wa a Ivory Coast.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nwokocha daga wasanni kan amfani da haramtattun ƙwayoyi

Najeriya mai kofin Afirka uku jimilla ta yi nasara a kan Kamaru karo na uku a babbar gasar tamaula ta Afirka da suka haɗu a bayan nan.

Super Eagles ta yi nasara a kan Indomitable Lions a zagayen quarter finals a 2004 da aka yi a Tunisia, sannan Najeriya ta doke Kamaru 3-2 a wasannin da aka gudanar a Masar a 2019.

Najeriya ta kawo matakin zagaye na biyu a Ivory Coast, bayan da ta yi ta biyu a rukunin farko da maki bakwai, iri ɗaya da na Equatorial Guinea, wadda ta yi ta ɗaya.

Super Eagles ta haɗa maki bakwai ne, bayan tashi 1-1 da Equatorial Guinea a wasan farko a rukuni na ɗaya da cin Ivory Coast 1-0 da kuma nasara a kan Guinea – Bissau 1-0.

Ita kuwa Indomitable Lions ta yi ta biyu ne a rukuni na uku, bayan da ta yi 1-1 da Guinea da rashin nasara 3-1 a hannun Senegal, sannan ta doke Gambia 3-2.

Kamaru mai Afcon biyar ta fara da lashe kofin Afirka a kan Najeriya a 1984 da cin 3-1 da kuma 1988 da ta yi nasarar cin 1-0 da kuma a 2000 da suka tashi 2-2, Kamaru ta lashe kofin a bugun fenariti 4-3 a Afirka ta Kudu.

Leave a Reply