Ƙasar Chaina za ta taimakawa Najeriya wajen gina tashar wutar lantarki

Daga Maryam Umar Abdullahi

Kamfanin makamashi na “Mainstream” a Najeriya, wanda tuni yake gudanar da manyan tashoshin samar da wutar lantarki guda biyu a ƙasar, ya fara gudanar da wani sabon ginin da ƙasar Chaina ta samar, kusan shekara guda bayan samun wannan damar in ji kamfanin a jiya.

Kamfanin makamashin “Mainstream Energy Solution Ltd” ya ce reshensa na Penstock Energy Ltd yana gudanar da sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 700 a garin Zungeru dake tsakiyar Najeriya, wanda aka gina da lamunin dalar Amurka biliyan 1.3 daga ƙasar Chaina.

Hukumar kula da kamfanonin gwamnati ta Najeriya, BPE, a watan Fabrairun da ya gabata, ta ba da rangwamen ga Mainstream Energy, wanda zai biya gwamnatin Najeriya dalar Amurka miliyan saba’in (70) daga nan har zuwa sama da shekaru 30 don ci gaba da ayyukan kamfanin.

KU KUMA KARANTA: Sama da mutane 70 ne suka mutu, sakamakon rugujewar mahaƙar Zinari a ƙasar Mali

A cikin shekaru goman da suka gabata, ƙasar Chaina ta taka rawar gani a Najeriya, inda ta samar da kuɗi ta bankin raya ƙasa don gina ababen more rayuwa da suka haɗa da layin dogo, filayen jiragen sama, da tashoshin samar da wutar lantarki.

Kamfanin samar da wutar lantarki na Kainji da Jebba da ke ƙarƙashin Mainstream Energy sun haɗa da megawatt 1338 wanda ya kai kusan kashi 33 cikin 100 na wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa a halin yanzu mai ƙarfin megawatt 4000.

Akwai buƙatar ƙari da yawa yayin da miliyoyin gidaje da wuraren kasuwancin ke ci gaba da fama da rashin wuta akai-akai.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *