No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce shugaban ƙasar ba shi da aniyar ɗauke babban birnin tarayyar ƙasar daga Abuja zuwa Legas.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (twitter), ranar Laraba, Onanuga ya ce masu yaɗa jita-jita ne ke yaɗa maganar domin jan hankalin al’umma gare su.

Wannan na zuwa ne bayan matakin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ɗauka na mayar da wasu ɓangarori na Babban bankin Najeriya da kuma Hukumar kula da filayen jiragen sama na ƙasar zuwa Legas, daga Abuja.

Lamarin da ya janyo ƙorafi da ƙiraye-ƙiraye daga wasu ƙungiyoyi na wasu ɓangarorin ƙasar, inda suka yi zargin cewa tamkar wani mataki ne aiwatar da wata ‘manufa ta daban.’

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta mayar da shalkwatar hukumar jiragen sama zuwa Legas

Onanuga ya ce matakin mayar da wani sashi na ma’aikatar FAAN bai kamata ya ja hankalin mutane da yawa ba saboda jihar Legas ita ce cibiyar kasuwanci kuma cibiyar sufurin jiragen sama a Najeriya saboda haka ya ce har yanzu FAAN za ta ci gaba da kasancewa a Abuja.

“Akwai ma’aikatu da yawa da ba a Abuja suke ba dangane da aikinsu kamar NIMASA da take Legas. Haka kuma NPA da kuma hukumar kula da sufurin ruwa (NIWA) da ke Lokoja.’

Sanarwar dai ta ƙara da cewa bai kamata a siyasantar da lamurran gwamnati ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...