Karim Benzema ya gurfanar da Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Gerald Darmanin a gaban kotu bisa zargin ɓata masa suna bayan da a bara ya yi zargin cewa tsohon ɗan wasan na Real Madrid yana da alaƙa mai girma da Ƙungiyar ‘Yan’uwa Musulmai.
Takardun ƙarar da Hugues Vigier, lauyan Benzema ya shigar ranar Talata sun bayyana cewa zargin da ministan ya yi masa sun zubar da kimar ɗan wasan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.
Ya gurfanar da ministan ne a Kotun Cour de Justice, wadda ita ce kaɗai take da ikon hukunta jami’an gwamnatin ƙasar bisa aikata laifi a yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Benzema, wanda Musulmi ne kuma yanzu yana murza leda a ƙungiyar Al Ittihad ta ƙasar Saudiyya, ya ce ba shi da alaƙa ko kaɗan da Ƙungiyar ‘Yan’uwa Musulmai, kuma ba shi da dangantaka da kowane ɗan ƙungiyar”.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta nemi taimakon Faransa kan matsalar tsaro
Ya ƙara da cewa: “Ina sane da yadda ake amfani da matsayina na shahararren mutum wajen cim ma buƙatu na siyasa, waɗanda suka ɗauki sabon salo tun bayan ranar 7 ga watan Oktoba.”
Darmanin, mai tsattsauran ra’ayi da ke son zama shugaban Faransa, ya soki Benzema bayan tsohon ɗan wasan na Faransa wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2022 ya wallafa sako a shafinsa na X a tsakiyar watan Oktoba inda ya nuna goyon baya ga Falasɗinawan Gaza da aka mamaye.
A sakon nasa, ya ce bai kamata Isra’ila ta riƙa yin musu luguden wuta ba.