IGP ya bada umarnin ba sani ba sabo a hanyar Abuja zuwa Kaduna

0
124

Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IG), Mista Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin a ƙara tura jami’ai a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon ƙaruwar fargaba a kan tsaro a hanyar.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce an tura dakarun ne domin inganta tsaro a yankin.

“Wannan na nufin yin amfani da fasahar ci-gaba da dabarun inganta hanyoyin samar da tsaro gaba ɗaya,” in ji shi.

Egbetokun ya umurci mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda (DIG) mai kula da ayyuka Mista Ede Ekpeji da ya kula da ma’aikatan da suka yi aiki a kan hanyar.

Shugaban ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar wa ‘yan kasa da matafiya tsaron lafiyarsu, domin ƙara yawan jami’an tsaro a kan hanyar zai zama daƙile masu aikata laifuka.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun dawo hanyar Abuja-Kaduna, sun sace matafiya 30

Ya bayyana buƙatar haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin yankin da abin ya shafa, ya kuma buƙaci jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan, da bayar da rahoton abubuwan da ake zarginsu da kuma bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro.

IG ya ce kokarin haɗin gwiwa yana da matukar muhimmanci wajen kiyaye tsaro da jin daɗin mazauna da matafiya a kan hanyar.

Ya kuma jaddada cewa matakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin ‘yan sanda na tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Leave a Reply