Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta kama mutum tara da ake zargin su da ƙwarewa wajen safarar ƙananan yara da sace-sace da kuma sayar da ƙananan yara.
Kazalika an ceto ƙananan yara bakwai daga hannun mutanen, in ji Kwamishinan ‘yan sanda na Kano.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya wallafa a shafinsa, ya ce Kwamishinan ƴan sandan jihar , Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar ta Bompai a ranar Alhamis.
Kwamishina Usaini Gumel ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da wasu ayyuka da hukumar leken asiri ta yi, inda aka gano tsawon lokacin da ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi suka yi a sassan jihohin Kano da Bauchi da Gombe da Legas da Delta da Anambra da Imo, aka kuma wargaza su.
KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga a Taraba sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa
Kazalika an ceto ƙananan yara bakwai daga hannun mutanen.
Kwamishinan ya bayyana cewa an sayar da wasu daga cikin yaran da aka ceto masu shekaru tsakanin uku zuwa takwas daga tsakanin N300,000 zuwa N600,000 dangane da shekarunsu.
Ana yawan samun ƙorafin satar ƙananan yara a wasu jihohin arewacin Najeriya kamar su Kano, inda har rundunonin ƴan sanda suka ce bincikensu ya gano cewa ana kai yaran ne kudancin Najeriya ana sayar da su.
Kwamishina Gumel ya ƙara da cewa, “Ta hanyar bincike mai zurfi da tawagar jami’anmu masu sadaukarwa suka yi ne aka gano ayyukan waɗannan ƙungiyoyin masu aikata laifuka da suka shafe sama da shekara 10 suna aiki”.
‘Yan sandan sun ce a ranar 15 ga watan Disamban 2023 ne wata tawagar ƴan sanda a lokacin da suke wani bincike da aka shirya yi a tashar motar Mariri da ke Kano, suka kama wata mata Comfort Amos mai shekara 45, a kan hanyarta ta zuwa Legas da wani yaro ɗan shekara biyar mai suna Abdulmutalib Sa’ad, ɗan unguwar Zango da ke Jihar Bauchi.
Wannan binciken ne ya jawo aka gano wasu karin mutane huɗu, lamarin da ya jawo har bincike ya dangana da Jihar Bauchi inda aka sake kamo wasu mutanen da ke safarar yara tsakanin Kano da Bauchi zuwa kudancin Najeriya.
“A cikin yaran da aka gano an sayar a yayin binciken har da wani yaro Mohammed Ilya, wanda aka sace daga Bauchi amma aka canza sunansa zuwa Chidebere a garin Nnewi da ke jihar Anambra,” in ji Gumel.
Ya ce rundunar ‘yan sandan za ta haɗa kai da gwamnatin jihar Kano domin ganin an dawo da dukkan yaran da aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da haɗuwa da ‘yan’uwansu na asali.
Kwamishinan ya tabbatar wa da jama’a cewa rundunar,a ƙarƙashinsa ta samar da matakan tsaro domin kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya.