Budurwa ta yi amfani da bindigar ɗan sanda ta harbe shi har lahira

Wani ɗan sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Cosmas Ugwu, ya gamu da ajalinsa bayan budurwarsa ta harbe shi har lahira.

An kashe Ugwu ne a ranar Talata, 26 ga watan Disamba, bayan  budurwarsa mai shekaru 23, wacce aka bayyana sunanta da Amanda Uchechi Ugo, ‘yar asalin ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo ta harbe shi.

An tattaro daga majiya mai tushe cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Disamba 26 a yankin Ezinihitte.

Marigayin ya yi faɗa da budurwar tasa a ɗakin da ke ofishin ‘yan sanda, kuma ana cikin rikicin ne sai yarinyar ta kai hannu ta ɗauki bindigar marigayin, ta ja bindigar ta harbe shi har sau uku.

KU KUMA KARANTA: Ɗan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya harbe kansa

An ce jami’an da ke bakin aiki sun gudu ne bayan da suka ji ƙarar harbe-harbe har sau uku. 

Wata majiya ta ce a ranar Alhamis: “Lokacin da jami’an ‘yan sanda suka shiga ɗakin daga baya don ganin abin da ke faruwa, sai suka tarar da Kofur Ugwu a kwance a cikin jininsa.  

Yarinyar ta harbe shi har sau uku a ƙirjinsa da kuma hannun hagu. Nan take aka garzaya da shi Asibitin Evergreen da ke Ezinihitte, inda Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsa.”

“A zahiri babu wanda ya san abin da ya faru tsakanin su biyun, amma yadda yarinyar ta yi nasarar amfani da bindigar ‘yan sanda cikin nasara har yanzu abin mamaki ne ga mutane da yawa, wataƙila Ugwu ne ya koya mata.”

An ajiye gawar jami’in da aka kashe a ɗakin ajiyar gawa na Obizi yayin da ake ci gaba da bincike.

Wanda ake zargin tana hannun ‘yan sanda.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan sanda na yin duk abin da ya dace domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *