’Yan bindiga sun ritsa mutane a kasuwar Gongon Maliki da ke ci duk ranar Laraba a Jihar Taraba, suka yi awon gaba da mutane da kayayyaki.
Ana tsaka da cin kasuwar a ranar Larabar nan ’yan bindiga kimanin 50 suka iso a kan babura, suka tare kofar kasuwar suka rika luguden wuta tare da gargaɗin kada wanda ya yi yunkurin ficewa daga kasuwar.
Daga nan suka yi ta tisa keyar ’yan kasuwa tare da kwace musu kuɗaɗe da kwasar kayan abinci da tufafi da sauransu, suka yi awon gaba da su.
Wakilinmu ya ruwaito cewa da misalin ƙarfe 12.30 na ranar Laraba ne ’yan bindigar suka kai farmaki a kasuwar da ke Karamar Hukumar Yorro ta Jihar Taraba.
KU KUMA KARANTA: An sace tsohon ciyaman da wasu mutum 10, an kuma kashe mutum 2
Aminiya ta gano cewa ’yan kasuwa da dama da suka zo cin kasuwar daga wasu wurare suna daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin garin mai suna Adamu, ya ce tafiyar maharan ke da wuya jama’a suka watse daga kasuwar, wasu ’yan garin kuma suka yi ƙaura.
Wakilinmu ya yi kokarin tuntuɓar kakakin ’yan sandan jihar, amma hakan bai yiwu ba.