No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ɗaruruwan ’yan kasuwa ne suka yi asarar ƙadarori na miliyoyin naira a wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Gwarzo da ke ƙaramar hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Gobarar ta ranar Litinin ta jefa ’yan kasuwa cikin ruɗani, inda wasunsu suka yi ta kokawa kan asarar babbar jarinsu.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce gobarar ta kone shaguna da dama ta lalata dukiyoyin miliyoyi na naira, amma ba a samu asarar rai ko wanda ya ji rauni ba.

KU KUMA KARANTA: Mummunar gobara ta jikkata mutane fiye da 80 a birnin Conakry

Ya bayyana cewa, gobarar ta tashi ne da tsakar daren Lahadi kuma sai dai jami’ansu sukai kai safiyar Litinin suna aiki kafin su kashe ta.

Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar da suka yi asara, Dayyabu Lawan Bala ya ce ya yi asarar ƙadarori na sama da miliyan biyar, ciki har da shagon.

Ya yi ƙira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...