No menu items!

Sample Page Title

Date:

A cikin kwanaki 10 mahara sun sace sama da mutum 10 a yankunan.

Alfijir labarai ta rawaito an sace tsohon Shugaban ƙaramar hukumar Yorro ta jihar Taraba, Mista Ishaya Dimas Dila tare da wasu mutum 10.

An sace tsohon shugaban ƙaramar hukumar ne da wasu mutane biyu a ƙauyen Dila da ke ƙaramar hukumar a ranar Lahadi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace manoma 11 a Abuja

Kazalika, ’yan bindiga sun harbe mutum biyu a ƙauyen Kunini da ke ƙaramar hukumar Lau.

Aminiya ta gano cewa an harbe mutanen biyu ne sakamakon turjiyar da suka yi wa ’yan bindigar.

Maharan sun kuma sake yin awon gaba da mutum takwas a ƙauyen Kunini duk a ranar Lahadi.

Bincike ya nuna cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata an sace mutane sama da 40 a ƙauyukan Dila, Pupule, Maraban Kunini da kuma Kunini da ke ƙananan hukumomin Lau da Yorro.

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ba a samu damar jin ta bakinsa ba game da lamarin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...