Ya kashe jami’in kotu kan kawo masa takardar sammaci

0
126
Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wani mutum mai shekaru 43 da aka kai wa takardar sammaci ya soka wa ma’aikacin kotun wuka ya kashe shi.

Mutumin ya yi wa akawun kotun wannan aika-aika ne a unguwar Kugama Wuro Jibir, ƙaramar hukumar Mayo Belwa da ke Jihar Adamawa.

Ma’aikacin kotun mai suna Yauba Usman ya kai masa takardar sammaci ne daga kotun yanki na Nasarao Jereng, amma mutumin ya ƙi karɓa.

A maimakon haka, sai mutumin ya zaro wuka ya rika soka wa ma’aikacin kotun, ya ji masa raunuka, lamarin da ya sa aka kai shi asibiti, amma rai ya yi halinsa.

KU KUMA KARANTA: Ɗan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya harbe kansa

Kakakin ’yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Nguroje ya ce a sakamakon haka rundunarsu ta cafke wanda ya yi wannan aika-aika, ana masa tambayoyi a ofishinsu.

SP Nguroje ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Afolabi Babata ya ba da umarni a zurfara bincike a kan lamarin.

Leave a Reply