No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan bindiga sun sace wani sarki mai daraja ta biyu tare da iyalansa da dogarinsa a ƙaramar hukumar Yorro a Jihar Taraba.

Sarkin mai suna Alhaji Umaru Abubakar Nyala an ɗauke shi ne tare da matarsa mai juna biyu da ɗansa da dogarinsa da wasu talakawansa a daren Litinin.

Har cikin fardar sarkin da ke garin Pupule ’yan bindigar suka shiga suka yi awon gaba da shi da iyalan nasa, in ji majiyarmu a garin Pupule.

Majiyar ta ce ’yan bindigan fiye da 20 ɗauke da manyan makamai ne suka afka wa garin a tsakar daren Litini suna ta harbe-harbe, wanda ya sa jama’a tserewa daga garin.

Daga bisani ne maharan suka kutsa kai zuwa cikin fadar sarkin suna ruwan wuta.

Majiyar ta ce sai da gari ya waye aka gane cewa an sace sarkin garin da iyalansa da wasu mutane masu yawa a garin.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga a Zamfara sun sace Hakimi da Limami

Wani mazaunin garin, Lawal mai doya, ya ce wannan shi ne karo na uku da ’yan bindiga suka kai garin suka sace mutane.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Taraba SP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar harin, amma ya ce har yanzu ba a ji ɗuriyar sarkin da sauran mutanen ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...