Aƙalla mutane 116 ne suka mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta ruguje gidaje a arewa maso yammacin ƙasar China, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito da safiyar Talatan nan, yayin da jami’an ceto suka dukufa wajen tona baraguzan gine-gine cikin wani yanayi mai sanyin gaske.
Jami’ai a lardin Gansu da lamarin yafi muni sun ce kimanin mutane 105 ne suka mutu sannan kusan 400 suka jikkata, sakamakon girgizar ƙasa mai karfin gaske da ta afku da tsakar dare.
Gidan talabijin na ƙasar CCTV, ya ruwaito cewar, a can birnin Haidong na lardin Qinghai mai makwabtaka kuwa girgizar ƙasa ta kashe mutane 11 tare da jikkata wasu 100.
KU KUMA KARANTA: An yi girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 3.6 a Ghana
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, girgizar ƙasar mai karfin maki 5.9 ta yi ɓarna sosai, da suka haɗa da rugujewar gidaje, tare da warwatsa bin titi domin neman tsira.
An fara aikin ceto da sanyin safiyar Talata, inda shugaban ƙasar Xi Jinping ya yi ƙira da aƙara azama a aikin ceto da kuma tabbatar da tsaron waɗanda suka tsira da kuma dukiyoyinsu.