Rikici ya kaure tsakanin Biden da Netanyahu kan hare-haren Gaza

0
90

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya kamata Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sauya tsattsauran ra’ayin gwamnatinsa inda ya ce nan gaba ba zai yiwu Isra’ila ta hana tabbatar da ƙasar Falasɗinu ba, sai dai Netanyahu ya yi raddi cewa Amurka ta jefa “bama-bamai masu guba” a Japan.

Biden ya yi tsokacin ne a wurin bikin tara masa kuɗi na yakin neman zaɓensa na 2024 bayan Amurka ta sayar wa Isra’ila tankokin yaƙi 14,000 ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ba sannan ta hau kujerar-na-ki lokacin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ya nemi amincewarta game da ƙudirin da ke neman Isra’ila ta tsagaita wuta a Gaza.

Biden ya ce “galibin ƙasashen duniya suna goyon bayan” Isra’ila, duk kuwa da zanga-zangar da ake ta gudanarwa a faɗin duniya na kyamarta tun daga 7 ga watan Oktoba sannan ƙasashe mambobin Kwamintin Tsaro na MƊD da ma mambobin Babban Zauren MDD sun yi tarayya wajen kira a kawo ƙarshen cin zalin da Isra’ila take yi wa al’ummar Gaza.

“Amma yanzu su (Isra’ila) sun soma rasa goyon baya saboda yadda suke kai hare-haren bama-bamai irin na kan mai-uwa-da-wabi,” in ji Biden.

KU KUMA KARANTA: Yaƙi tsakanin Isra’ila da Falasɗinu, Rasha da Ukraine ya shafi tallafin kuɗin kiwon lafiya a Afirka – UNICEF

Biden ya yi waɗannan kalamai ne a yayin da mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro, Jake Sullivan, yake shirin tafiya Isra’ila domin tattaunawa da majalisar da ke aiwatar da yaƙi ta ƙasar.

Biden ya ambaci ɗan siyasar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir, wanda shi ne ministan tsaron ƙasa na Isra’ila, inda ya ce “wannan ce gwamnati mafi tsattsauran ra’ayi a tarihin Isra’ila.”

“Ya kamata [Netanyahu] ya canza gwamnatinsa. Wannan gwamnatin ta Isra’ila tana sanya abubuwa suna yin tsauri,” a cewar Biden. Ya ce nan gaba ba zai yiwu Isra’ila “ta ƙi yarda” a kafa ƙasar Falasɗinu ba, matakin da masu tsattsauran ra’ayi na Isra’ila suke adawa da shi.

Biden ya yi tsokaci a game da wata kevantacciyar hira inda firaministan Isra’ila ya ce: “‘Ku [Amurkawa] kun jefa bama-bamai a Jamus, kun jefa bama-bamai masu guba da suka kashe ɗimbim ƙananan yara.'”

Biden ya ce ya mayar da martani da cewa: “Eh, haka ne shi ya sa bayan Yaƙin Duniya na Biyu aka samar da tsare domin ganin irin wannan bai sake faruwa ba… kada ka maimaita kuskuren da muka lokacin harin 9/11. Babu wani dalili da ya sa muka yi yaki a Afghanistan.”

Leave a Reply