An kama mutane uku da ke tone gawarwaki a kabari

0
133

Rundunar Amotekun Corps a jihar Osun ta kama wasu mutane da suka ƙware wajen tono gawarwaki tare da cire sassan jikinsu domin yin tsafi.

A wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, mai magana da yawun Amotekun na jihar Osun, Adeniyi Adeshola Brown, ya ce mutanen ukun sune; Kamilu Kehinde mai shekaru 43 mai sana’ar kanikanci da Akeem Hamzat direba mai shekaru 56 da kuma Wakeel Baka mai sana’ar tsibbu.

Brown ya bayyana cewa an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da jami’an rundunar Iwo suka samu.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama matsafa biyar masu tono gawarwaki

Ya ce: “A yayin da ake yi musu tambayoyi, waɗanda ake zargin sun yi iƙirarin cewa suna cikin harkar tono gawarwaki daga kaburbura; wanda sai su sayar wa masu saye da suke bukatarsu domin yin tsafin neman kuɗi”.

Kakakin, ya bayyana cewa kwamandan rundunar ta jihar Osun, Bashir Abiodun Adewinmbi, ya bayar da umarnin a miƙa waɗanda ake zargin zuwa rundunar ‘yan sandan Najeriya domin gudanar da bincike na gaskiya da kuma gurfanar da su gaban ƙuliya.

Leave a Reply