Kotu ta tilasta gwamnatin Kano biyan diyyar rusau

0
141

Babbar Kotun Tarraya ta ba da umarnin wucin gadi da ke tilasta Gwamnatin Kano biyan diyyar naira biliyan 30 ga ’yan kasuwar da ta yi wa rusau a filin idi.

Kotun da ke zamanta a Kano ta buƙaci ɓangaren gwamnatin ya bayyana a gabanta domin ta ji ko suna da dalilin da zai hana aiwatar da umarnin nata.

Mai shari’a I.E. Ekwo na kotun ya ba da umarnin ne kamar yadda takardar hukuncin, ɗauke da sa hannu magatakardan kotun, Chioma Chijioke, ya nuna, mai ɗauke da kwanan watan 28 ga Nuwamba, 2023

Sabon umranin kari ne a kan wanda Mai Shari’a S.A Amodeba J ya bayar a watan Satumba ga ƙungiyar ’yan kasuwar filin idi da wasu mutane da kamfanoni da suka shigar da ƙarar neman diyya saboda rushe dukiyoyinsu da gwamantin ta yi a watan Yuni.

“Naira biliyan 30 za a biya daga duk kuɗaɗen Gwamnatin Kano da ke bankuna da waɗanda ta ke samu daga Gwamnatin Tarayya da na sauran asusun ajiyar waɗanda ake ƙara, kamar yadda Mai Shari’a S.A Amodeba J, ya ba da umarni ranar 29 ga watan Satumba, 2023,” in ji sabuwar hukuncin kotun.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ci tarar Gwamnan Kano N25m kan zargin Alhassan Doguwa da kisa

Ta ƙara da , “umartar waɗanda ake ƙara da su bayyana a gabanta, ta ji ko suna da dalilin da zai hana aiwatar da umarnin biyar diyyar.

“Masu ƙarar za su ba wa waɗanda ake ƙarar takardar hukuncin aƙalla kwanaki 14 kafin zama na gaba,” in ji Jastis Ekwo.

Sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairu, 2024 domin gwamnatin ta kare kanta.

Hakan na nufin idan gwamnatin ta ƙi zuwa ko ta kasa kare kanta, to kotun za ta ba da umarnin cirar naira biliyan 30 ɗin daga asusun ajiyarta da ke bankuna.

Idan abin da ke take da shi a banki bai kai baira biliyan 30 ba kuma, to za a rufe su, duk kuɗaɗen da suka shiga za a cire, har sai an gama cire kuɗaɗen.

Yanzu abin jira a ganin shi yadda za ta kaya.

Leave a Reply