Kotu ta sake ɗage sauraron shari’ar kisan Ummita zuwa 2024

0
172

Bayan wata bakwai babu zaman kotu, an sake ɗage sauraron shari’ar ɗan Chinan da ake zargi da kisan budurwarsa Ummulkusum Buhari (Ummita) a Kano zuwa shekarar 2024.

A jiya laraba ne aka ci gaba da sauraren shari’ar ɗan ƙasar Chinan Mista Frank Quangrang Geng, wanda gwamnatin Kano ta gurfanar bisa zarginsa da kisan budurwarsa Ummita a jihar.

Shari’ar da da ake yi tsakanin Gwamnatin Jihar da ke ɗan ƙasar Chinan ne bayan shafe watanni bakwai ba tare da zaman shari’ar ba, saboda shari’o’in zaɓe.

A zaman, Lauyan ɗan China Barista Muhammad Ɗan azumi ya nemi afuwar kotun bisa rashin kawo rubutaccen bayanansa na ƙarshe daga ɓangarensu, sakamakon ayyukan shari’oin zaɓe da suka ɗauke masa hankali.

“A yanzu haka na kusa kammala rubuta bayanaina na ƙarshe, zuwa makon gobe zan kammala sannan in mika wa ɓangaren masu ƙara,” kamar yadda ya shaida wa kotu.

KU KUMA KARANTA: An tsayar da ranar ci gaba da sauraron shari’ar ɗan China da Ummita

Sai dai lauyan gwamnati, Barista Aisha Mahmud, ta yi suka game da wannan bayani na ɓangaren waɗanda ake ƙara.

Amma ta ce babu yadda za su yi, “Yanzu dole sai mun jira sun kammala rubuta bayanansu na ƙarshe sannan mu kuma mu bayar da amsa. Daga karshe kuma sai a yanke hukunci,” in ji ta.

Ta kuma nemi kotu da ta ja hankalin lauyan wanda ake ƙara da su mayar da hankali kan shari’ar duba da yanayin kes din wanda ya shafi kisan kai.

Alkalin kotun, Mai Shari’a, Sanusi Ado Ma’aji, ya ɗage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Janairu 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here