No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da aƙalla mutum bakwai a ƙauyen Igu da ke yankin Sherefe a ƙaramar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne da daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Yahaya, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun isa unguwar ne a lokacin da mutane suka shiga masallaci domin yin sallar magariba.

Yahaya ya ce an yi awon gaba da mutum bakwai, sannan maharan sun harbi mutum ɗaya da bindiga.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan da aka sace wani hakimin yankin, Chebawaza Sariki, amma daga baya aka sako shi a daren Asabar.

Haka kuma, kimanin wata guda, an sace mutum biyu a wasu yankuna biyu na Sherefe.

A baya-bayan nan hare-haren ’yan bindiga na ci gaba da ƙamari a wasu yankunan birnin tarayya, Abuja.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...