No menu items!

Sample Page Title

Date:

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, an samu raguwar mace-mace sakamakon cutar AIDS da kashi 70 cikin 100 a faɗin duniya tun 2004.

Majalisar ta ce duk da wannan matsayi da aka cimma, har yau AIDS na kashe mutum guda a cikin duk minti guda.

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ne ya bayyana haka cikin saƙon da ya fitar albarkacin Ranar Yaƙi da AIDS ta Duniya ta 2023.

António Guterres ya ce, “ya zama wajibi mu ga bayan AIDS a matsayin ƙalubale ga lafiyar al’ummar duniya ya zuwa 2030.”

Ya ƙara da cewa, domin kawar da AIDS dole ne a mayar da hankali kan ƙauyuka wajen ba su kulawar da ta dace game da kiwon lafiya da dai sauran tallafi.

KU KUMA KARANTA: Kimanin Yara Miliyan 13 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Najeriya – UN

Haka nan, ya ce don cimma nasarar yaƙi da HIV ya zama dole a tafi tare da shugabanni al’ummomin karkara wajen gudanar da harkokin yaƙi da cutar.

Ya ce ana buƙatar sama da Dala biliyan takwas duk shekara wajen yaƙi da wannan cuta a ƙasashe masu samun ƙarami da matsakaicin kuɗin shiga.

“Lallai kawar da AIDS abu ne mai yiwuwa. Mu ƙarasa aikin kawar da cutar ta hanyar tallafa wa ’yan karkara wajen yaƙi da wannan cuta,” in ji António Guterres.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...