No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da yi wa ’yar shekara biyu fyaɗe a hihar Adamawa, ya ɗora alhakin ta’adar da ya aikata a kan barasa.

Mutumin mazaunin ƙauyen Aljannaru da ke ƙaramar hukumar Song, ya shiga hannun jami’an ’yan sanda a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Sai dai mutumin a yayin shan titsiye, ya ce ya yi aika-aikar ne sanadiyyar mankas a dalilin barasa da ya yi tatul da ita.

A cewarsa, a ranar da lamarin ya faru, ya sha wata barasa mai suna Voltage, wadda ta jefa shi cikin yanayi na matsananciyar sha’awa da ya kasa jurewa har ya zakke wa ƙaramar yarinyar.

KU KUMA KARANTA: Tsoho mai shekara 70 ya yi wa yarinya kurma yar shekara 15 fyaɗe har ta mutu

Aminiya ta ruwaito cewa, wata yayar yarinyar ce ta kama shi yana tsaka da masha’a da kanwarta, lamarin da ya kai ga cafke shi kuma a miƙa shi hannun ’yan sanda.

A yayin bincike, an gano cewa mutumin magidanci ne da matarsa wadda a yanzu haka ma tana da juna biyu.

Tuni dai Kwamishinan ’Yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike a kan lamarin sannan a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...