No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a jihar Enugu ta tasa ƙeyar wani tsoho mai shekaru 70, Anthony Mgbe zuwa gidan yari bisa zargin laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara 15.

Wanda aka kashen mai suna  Uchechukwu Onwuzuru, wanda aka ce kurma ce kuma bebiya, ta zubar da jini har ta mutu bayan da wanda ake zargin ya yi mata fyaɗe.

KU KUMA KARANTA: An yi wa budurwar da ta yi tatil da giya fyaɗe a Ogun

Tsohon ya fito daga Umuagu, ƙaramar hukumar Inyi Oji-River a jihar, an kama shi ne a kan tuhume-tuhume biyu da ’yan sanda suka yi masa.

Bisa la’akari da girman laifin, kotun majistare ta ƙi amincewa da bukatar neman belin tsohon ta kuma ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba, 2023.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...