Hisbah ta cafke mutum 37 kan karuwanci da sayar da giya a Yobe

0
167

Rundunar haɗin gwiwar Hisbah da ’yan sanda da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta cafke wasu mutane 37 bisa zargin su da yin karuwanci da sayar da giya a Damaturu babban birnin Jihar Yobe.

Muƙaddashin kwamandan Hisbah na jihar, Mohammed Murtala Goni Ahmed, ya ce an kama mutanen ne a Zango, Maina Lodge, Ajayi, Bakin Kasuwa da kuma Bakin Tasha a Damaturu.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ofishin rundunar ’yan sandan jiar, ya bayyana cewa mata 17 da maza 20 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 18 suka shiga hannu a samamen.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta kori jami’inta kan haɗa kai da masu baɗala a Kano

“Binciken da aka gudanar a kan waɗanda ake zargin ya kuma nuna cewa, a cikin mazan, an same su da yawa suna sayar da ƙwayoyi sannan kuma an same su da kiret 50 na kwalaben giya,” in ji Goni.

Wasu daga cikin waɗanda ake zargin da suka zanta da Aminiya sun ce an kama su ne bisa kuskure domin ba su da laifin abin da ake zargin su da shi.

Leave a Reply