Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gayyaci jarumai da furodusoshi da darakatocin fina-finan Hausa na Kannywood, mako guda bayan ta gana da ’yan TikTok.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah (ɓangaren ayyuka), Dokta Mujahideen Aminudden ya bayyana cewa hukumar na son ganawa da ’yan Kannywood ne don tattaunawa a kan abin da ya shafi gyaran sana’arsu.
Dokta Mujahideen ya ce kamar yadda aka samu fahimtar juna hukumar da ’yan TikTok a makon da ya gabata, suna sa rai tattaunawar da ’yan fim zai haifar da kyakkyawan sakamako.
“Muna neman jarumai da masu shirya fiina-finai da masu bayar da umarni, da duk wasu da ke yi wa fim hidima ban da mawaka.
KU KUMA KARANTA: Hisbah ta kori jami’inta kan haɗa kai da masu baɗala a Kano
“Muna sa rai tattaunawar tamu za ta haifar da alheri kamar yadda waccan tattaunawarmu da ’yan TikTok”
Sai dai ƙungiyar Jarumai ta Kannywood ta nuna rashin jin dadinta game da hanyar da Hisbar ta bi wajen gayyatar su inda ta nemi Hisbar da ta gyara kuskuranta.
Shugaban ƙungiyar, Alhasan Kwalle, ya bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da za su yi zama da Hisbah ba, don haka suna maraba da gayyatar.
“A lokutan baya mun zauna da Hukumar Hisbah inda suka ba mu shawarwarin a kan sanaarmu.
“Sai dai a wannan karon maimakon Hisbar ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar tamu, amma sai muka tsinci sanarwar a rediyo, wanda a ganinmu hakan ya yi kama da neman masu laifi.
“Kamata ya yi Hukumar Hisbah ta aiko mana da takarda ko kuma ta neme mu ta hanyar Hukumar Tace Finafinai. Muna da ƙungiyoyi daban-daban wanda kuma akwai babbar ƙungiyarmu,” in ji shi.
Ya ce duk da hakan masu ’yan fim ɗin za su amsa ƙiran kamar yadda ta nema inda ya ce a “yanzu ma a shirye muke mu amsa gayyatar Hukumar muddin dai Hukumar za ta gyara kuskurenta.“