Kotu ta dakatar da ƙugiyoyin ƙwadago tafiya yajin aiki da suka shirya

0
238

Kotun ɗa’ar ma’aikata ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC daga shiga yajin aikin da suka shirya yi a ranar talata.

Alfijir Labarai ta rawaito Alƙalin kotun, mai shari’a Benedict Kanyip ne ya bada umarnin dakatar da yajin aikin bayan ƙarar da gwamnatin Najeriya da ministan shari’ar ƙasar suka shigar gaban kotun, don neman kotun ta hana su shiga yajin aikin, saboda hakan zai iya jefa ‘yan ƙasar cikin ƙarin wahala.

Lauyan masu gabatar da ƙarar Barista Tijani Gazali ya ce matsawar ba a dakatar da ƙungiyoyin daga shiga yajin aikin ba, za a iya samun tayar da hargitsi tare da kawu ruɗani a faɗin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya za su tsunduma yajin aiki

Yayin da yake hukuncin, alƙalin kotun ya ce, kotun na da hurumin shiga tsakani domin hana duk wani abu da ka iya tayar da hankula a ƙasar.

Mai shari’a Kanyip ya yi amfani da sahe na 17 da 19 na ƙundin dokokin kotun wajen dakatar da yajin aikin.

Leave a Reply