MƊD ta koka kan yadda matsin rayuwa ke ƙara tsanani a Sudan

Yayin da ƙazamin faɗa da ake gwabzawa a yankin Darfur ke ƙara tsanani tare da tilasta wa dubban ‘yan Sudan barin matsugunansu, akwai bukatar a ƙara kaimi wajen rage raɗaɗi da kuncin rayuwa da miliyoyin ‘yan ƙasar suka faɗa ciki, kamar yadda wani jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Cikin watanni shida an tilasta wa mutane miliyan shida yin ƙaura, wato kusan mutane miliyan ɗaya ne suke tserewa daga gidajensu a kowane wata, suna fuskantar ƙunci rayuwa ,” in ji Mamadou Dian Balde, babban jami’in yanki na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR).

Faɗan da ake gwabzawa tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) na Janar Mohamed Hamdan Daglo ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da mutum 9,000 tun daga watan Afrilu, a cewar wani rahoton MƊD.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

A cikin kusan mutane miliyan shida da suka yi gudun hijira, miliyan 1.2 daga cikinsu sun bar kasar, “mutane masu kima wadanda a yanzu suka tsinci kansu cikin yanayin bara” kuma rayuwarsu ta faɗa cikin ”garari baki daya,” in ji jami’in na MƊD.

Jami’ain ya yi gargaɗin cewa, yayin da hankalin duniya ya karkata zuwa ga yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, adadin mutanen da ke ƙaurace wa matsugunansu a Sudan ya ƙara yawa, yayin da dakarun RSF suka faɗaɗa kai hare-hare zuwa Nyala, birni na biyu da ke tsakiyar Darfur.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *