An tsinci gawar wata malamar sashen Biochemistry na Makarantar Kimiyyar Rayuwa ta Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) Minna a Jihar Neja, Dakta (Misis) Adefolalu Funmilola Sherifat da aka yanka a gidanta da ke Unguwar Gbaiko a garin.
Channels TV ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar malaman jami’a (ASUU) a makarantar Farfesa Gbolahan Bolarin ya ce, an gano gawar marigayiyar ne a safiyar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, lokacin da mabiya cocin ta suka bi ta gidanta bayan ba a gan ta a lokacin hidimar ibada ba.
Wasu mazauna garin sun ce bayan da aka buɗe ƙofar gidanta, an same ta a cikin jininta kuma an yi mata yankan rago a maƙogwaronta da wuƙaƙe a gefenta. Daga baya hukumomin ‘yan sanda sun ɗauke gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa.
KU KUMA KARANTA: An kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata, ta hanyar yi mata yankan rago a Gwambe
Kafin rasuwarta, tana zaune tare da wata mai yi mata hidima, amma ta sallami yarinyar a ranar Juma’a, 27 ga Oktoba.
Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba kafin lokacin rubuta wannan rahoto.









