No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ana fargabar cewa wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kashe wasu ma’aurata da wani malamin makaranta a ƙauyen Maro da ke ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Lamarin kamar yadda wakilinmu ya ruwaito, ya jefa mazauna yankin na Unguwar Ɗorawar Bakhira cikin firgici, yayin da malamin da lamarin ya rutsa da shi mai suna Mista Sunday Akorh, ya kasance malamin firamare daya tilo a kauyen.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, babu wanda aka samu rahoton cewa an yi awon gaba da shi a yayin harin da ’yan ta’addan suka kai da misalin ƙarfe 1:30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi.

Wani mazauni kuma jagoran al’umma a yankin, Maigari Ben, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantarwarsa da Aminiya a wannan Lahadin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace mata biyar da suka tafi biki a Katsina

“Sun kashe wani mutum da matarsa da wani malamin firamare mai suna Mista Sunday Akorh ɗan asalin jihar Benuwe.

“Malamin shi kaɗai ne yake koyarwa a wata makarantar firamare a wannan ƙauyen. Sai dai babu wanda aka yi garkuwa da shi,” a cewarsa.

Sai dai ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin jami’in hulɗa da rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Manir Hassan ya ci tura a yayin da ba a same shi a wayarsa ba, sannan kuma bai bayar da amsar saƙon kar ta kwana da aka tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...