Magidanci a Kano, ya yi ƙorafi kan mahaifin matarsa na yunƙurin kashe masa aure

0
171

Kotun Shari’ar Muslunci, da ke zaman ta a harabar Hukumar Hisbah a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Sani Tanimu Sani Hausawa, ta yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci ga wani miji kan ya maida matarsa da su ke tare shekaru goma da su ka gabata.

Mijin dai na zargin wani hakimi a jihar, wanda shi ne mahaifin matar ta sa, da ƙoƙarin kashe musu aure sakamakon mijin ‘yar ta sa ya yi mata kishiya, inda su kuma ‘ya’yan sarauta ba a yi musu kishiya.

Tun da fari, matar ce ta kai mijin nata ƙara zuwa kotun, inda take neman a kotu ta yanke igiyar auren na ta da mijin ta saboda ya ƙara aure.

KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum

A nan ne lauyan wanda ake ƙara, Barista Umar Yusuf Khalil, ya roƙi kotu da ta basu damar sulhu kasancewar sun kwashe shekaru 10 tare kuma suna da ‘ya’ya huɗu.

A cewarsa, shi aure rai ne da shi sai lokacin da Allah ya yi zai mutu, zai mutu, saboda haka su ke neman kotu ta sahale wa mijin ya mayar da matarsa, wacce ta shafe shekara ta na yaji a gidan mahaifinta.

Shi kuma lauyan mai ƙara, Barista Ibrahim Umar, ya shaidawa kotun, cikin yanayi na barkwanci, cewa idan wanda ake ƙara ya je yin biko, to ya tafi da daƙwalen kaji.

Sannan kuma ya musanta zargin cewa mahaifinta ne ya umarce ta da tafi gida domin gidansu na sarauta ne, kuma ba a yi wa ‘ya’yan gidan kishiya.

Ya kuma nuna cewa wanda ya ke ƙara na samun matsala ne da mai ƙara, inda ta gaji da zaman shi ne ta garzaya kotun don neman a raba auren.

Daga bisani kotun kuma ta amince da hakan sannan ta sanya ranar 20 ga watan Nuwamba don sake zaman shari’ar.

Leave a Reply