No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kotu ta tsare wata matar aure a gidan gyaran hali kan zargin kashe jaririn kishiyarta ta hanyar shayar da shi maganin ƙwari a jihar Kano.

Kotu ta tisa ƙeyar wata matar aure zuwa gidan yari kan zarginta da kashe jaririn kishiyarta a Jihar Kano.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf Ali na Babbar Kotun jihar Kano Mai lamba 16 ne ya ba da umarnin bayan gurfanar da matar auren daga ƙaramar Hukumar Ƙunci bisa zargin kisan jaririn.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure mutumin da ya damfari surukarsa akan zai saka Buhari ya aureta

Mai gabatar da ƙara, lauyan gwamnatin jihar, Barista Abba Lamiɗo Soronɗinki ya shaida wa kotun cewa matar ta kashe jaririn ɗan kimanin kwana 18 ne ta hanyar shayar da shi maganin ƙwari, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Bayan sauraron jawabin, alƙalin kotun, Mai shari’a Zuwaira Yusuf Ali ta bayar da umarnin tsare wacce ake zargin a gidan yari har zuwa ranar 2 ga watan Disamba 2023 don ci gaba da sauraren shari’ar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...