Hukumar kula da gasar firimiya ta Nigeria a ranar Litinin ta ci tarar Kano Pillars kuɗi har Naira miliyan ɗaya, sakamakon kutsen da magoya bayansu suka yi a filin wasa, a wasan da suka fafata da Rivers United.
An tabbatar da cewa magoya bayan ƙungiyar Kano Pillars sun ƙetara shingen filin wasa domin murnar cin ƙwallon da suka yi a minti na 92 a karawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha.
Bayan nazarin rahotanni daga jami’an wasan, hukumar kula da gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL ta tuhumi kulob ɗin da laifin karya doka mai lamba B13.18. Ta hukumar.
Don haka an umurci kulob ɗin da ya biya tarar cikin kwana 14, kuma ya ja kunne kan hakan, wanda gaza yin hakan zai zamo tamkar ci gaba da saɓa wa dokokin hukumar ta NPFL.