Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’a albashin watannin da suka yi suna yajin aiki

0
198

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin biyan malaman jami’an jami’o’i ƙarƙashin ƙungiyar ASUU albashinsu na watanni 8 da aka riƙe musu yayin yajin aikin bara.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen ranar Juma’a.

Ya ce Tinubu ya ɗauki matakin ne a ƙarƙashin shirinsa na yin yafiya da nuna tausayi.

Ajuri ya ce tun da suka umarci ma’aikatar Ilimi da ta ƙwadago da su yi aiki tare wajen aiwatar da umarnin, kodayake ya ce wannan shi ne zai zama karo na ƙarshe da gwamnatin za ta janye dokar ga ASUU da sauran ƙungiyoyin da ke ɓangaren ilimi.

Sai dai ya ce umarnin biyan albashin na watanni huɗu ne kawai daga cikin watanni takwas ɗin da suke bi.

KU KUMA KARANTA: ASUU za ta ware rana ɗaya don yin zanga-zangar lumana

A bara ne dai ASUU ta yi yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabrairu har zuwa 17 ga watan Oktoban 2022.

Sai dai a lokacin, gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta dakatar musu da albashin watannin da suka yi yajin aiki na takwas, inda ta fito da dokar “Ba aiki, ba albashi”.

Leave a Reply