No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mai suna Lekan Sunday bisa zargin yi wa wata malamar addini fyaɗe a wata coci da ke jihar.

An ce wanda ake zargin ɗauke da makami, ya kutsa cikin cocin Orioke Aanu Oluwa Gbohunmi da ke unguwar Ilogbo Adu da ke Kemta a Abeokuta, inda ya yi barazanar kashe Malamar idan ba ta ba shi haɗin kai ba, kuma ya sanya wuƙa a fuskarta.

Ana zargin Malamar ta fara roƙon mai laifin amma ya ƙi. Daga bisani ya yi mata fyade a cikin cocin.

Rundunar ‘yan sandan ta ƙaddamar da farautar wanda ake zargin da ya gudu, bayan ta samu ƙorafi daga Malamar addinin.

KU KUMA KARANTA: Mahaifi ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 13 fyaɗe

PUNCH ta ruwaito jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Odutola ya ce. Malamar addinin ta gane wanda ake zargin mesin ne kuma lebura a yankin.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da wanda ake zargin yake amsa tambayoyi a wajen ‘yan sanda.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...