Gwamnan Kano ya rattaɓa hannu kan naira biliyan 59 a matsayin kasafin kuɗi na 2023

0
258

“Wannan ƙarin kasafin kuɗin an yi shi ne domin a kula da ci gaban ababen more rayuwa na shekarar 2023, domin biyan buƙatun al’ummar jihar Kano.”

An rawaito Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan kasafin kuɗin na shekarar 2023 wanda ya kai biliyan hamsin da takwas, miliyan ɗari da casa’in da ɗaya, da dubu ɗari biyar da talatin da biyar, naira goma sha takwas, kobo goma sha biyu (N58,191, 535, 018.12).

Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa gwamnatinsa za ta bi ƙa’idojin kula da kasafin kuɗi domin kuɗaɗen da aka ware za su yi amfani da su cikin gaskiya da adalci.

“Wannan ƙarin kasafin kuɗin an yi shi ne domin a kula da ci gaban ababen more rayuwa na shekarar 2023, domin biyan buƙatun al’ummar jihar Kano.” Gwamnan ya bayyana.

KU KUMA KARANTA: NUJ Kaduna, Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Horar Da Mambobin Kungiyar

Gwamnan ya yaba da ƙoƙarin kwamishina, tsare-tsare da kasafin kuɗi na gaggawar aiwatar da takardar kasafin kuɗin ga majalisar jiha.

Tun da farko, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Jibrin Ismail Falgore wanda ya jagoranci manyan hafsoshi na majalisar kwamitin rabon kuɗaɗen ne ya gabatar da ƙudirin amincewar gwamnan a gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamnan ya kuma buƙaci a ci gaba da samun goyon baya da kyakyawar alaƙa tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisar dokoki a jihar Kano.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kano ya sanyawa hannu a ranar juma’a.

Leave a Reply