Gwamnatin Kano ta haramta amfani da wasu litattafai a ɗaukacin makarantun jihar

0
250

Gwamnatin Kano ta haramta amfani da wasu litattafai a ɗaukacin makarantu masu zaman kansu dana sakai a faɗin Jihar.

Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito hakan ya biyo bayan tunatarwa da ɓangarorin daban-daban sukai kan wasu illoli da suke cikin Litattafan da ake ganin sun ci karo da koyarwar Islama.

Hukumar Kula da makarantu masu zaman kansu ta fitar da sanarwar mai ɗauke da sa hannun Hamisu Muhammad, Daraktan tsare-tsare da bincike a Madadin Mataimakin Gwamna kan Makarantu Masu Zaman Kansu Baba Abubakar Umar.

Litattafan sune kamar haka:

*The Queen Primer (all editions) A Royal Series Published by Nelson Publishers Limited

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano za ta gina gadar sama da ta ƙasa, a wasu muhimman wurare a jihar

*Basic Science for Junior Secondary School, Razat Publishers, 2018 edition. (for JSS3).

*Active Basic Science, 2014 edition By Tola Anjorin, Okechukwu Okolo, Philias Yara, Bamidele Mutiu, Fatima Koki, Lydia Gbagu.

*Basic Science & Technology for Junior Secondary Schools 1, 2 and 3: By W.K Hamzat, S. Bakare.

*New Concept English for Senior Secondary Schools for SS2, Revised edition (2018 edition) by J Eyisi, A Adekunle, T Adepolu, F Ademola Adeoye, Q Adams and, J Eto.

*Basic Social Studies for Primary Schools by BJ Obebe, DM Mohammed, S N Nwosu, J A Adeyanju and ah Carbin

Bugu da ƙari shugaban Hukumar tace Fina-Finai da ɗab’i ta jihar Kano, Abba Al Mustapha sun yi nasarar kama tarin Littafin Queen Primer da Gwamnatin ta haramta koyar da shi a faɗin jihar Kano.

Leave a Reply