Rundunar sojin Faransa za ta fara kwashe dakarunta daga a jamhuriyar Nijar

0
221

‘Yan ƙasar Nijar sun kwashe wata da watanni suna gudanar da zanga-zangar ƙyamar Faransa da neman ta kwashe dakarunta daga ƙasar.

Alfijir Labarai ta rawaito Rundunar sojin Faransa ta bayyana cewa za ta soma kwashe dakarunta daga Jamhuriyar Nijar a wannan makon bayan dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.

“Za mu soma kwashe dakarunmu a wannan mako, a cikin tsari, tare da haɗin gwiwar ‘yan ƙasar Nijar,” a cewar sanarwar da hedikwatar rundunar sojin ta fitar ranar Alhamis.

KU KUMA KARANTA: Jakadan Faransa a Nijar ya isa gida

Ranar 24 ga watan Satumba Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta kwashe dukkan dakarunta 1,400 da jakadanta da ke Nijar nan da ƙarshen shekarar 2023.

Ranar Talatar da ta wuce Jakada Sylvain Itte ya fice daga ƙasar wata guda bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sun ba shi wa’adin awa 48 ya bar ƙasar bayan “ya ƙi amsa gayyatar ma’aikatar harkokin waje don halartar taron” da aka gayyace shi da kuma “wasu matakai da Faransa ta ɗauka da suka ci karo da muradan Nijar”.

Faransa ta jibge dakarunta a Nijar ne domin yaƙi da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu alaƙa da Al Qaeda da Islamic State da suka addabi yankin Sahel.

Ƙasar ta aika sojojinta kusan 400 su yi aiki da sojojin Nijar a kan iyakar ƙasar da Burkina Faso da Mali don murƙushe masu tayar da ƙayar baya.

Hedikwatar sojin Faransa ta ce sojojinta suna buƙatar tsaro, ciki har da kariya ta sama, kafin su fita daga sansaninsu don ficewa daga Yamai, babban birnin Nijar.

Dakarun Faransa sun faɗa cikin halin rashin tabbas tun bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka umarci su fice daga ƙasar, inda ba sa samun isasshen abinci sannan dubban ‘yan Nijar sun yi wa sansaninsu tsinke suna neman su fita daga ƙasar.

Dakarun na Faransa suna da zaɓi biyu ne na fita daga Nijar, ko dai ta ƙasar Benin, ko kuma ta Chadi saboda Nijar ta haramta wa jiragen Faransa shiga sararin samaniyar ƙasar.

Faransa ta ƙara yawan dakarunta a Nijar bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun kore ta daga can, inda ta aika ƙarin jiragen helikwafta da jirage marasa matuƙa da jiragen yaƙi.

Leave a Reply