Jama’a na ta alhinin rasuwar jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola

0
244

Daga Ibraheem El-Tafseer

A wayewar ranar Laraba ne aka tashi da labarin rasuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola Katsina. Rahotanni sun tabbatar da cewa, Hajiya Binta Ola ta rasu ne sakamakon gajeruwar rashin lafiya.

Jaridar Katsina Times, ta ruwaito cewa Hajiyan ta shirya taron Maulidi a wannan rana ta Laraba kamar yadda ta saba kowace shekara, inda ita da kanta ta dinga buga waya a mutane, tana gayyatarsu. Amma cikin dare jinyar ajali ta same ta, ta rasu. Duk wanda ya zo taron Maulidi, sai dai ya tarar da gawarta.

KU KUMA KARANTA: Yanzu yanzu; Rasuwar daraktan izzar so, Nura Waye

“An yi sauƙar alƙur’ani kamar yadda aka saba, a washegarin ranar da za ta yi Maulidi, aka raba musu abinci. Amma cikin dare Allah ya mata rasuwa” inji babbar ‘yarta.

Tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin musulunci ya karantar. An yi jana’izarta a ƙofar gidanta da ke Ƙofar Ƙaura cikin birnin Katsina.

Leave a Reply