Kotu a Amurka ta umarci jami’ar Chicago ta bai wa Atiku damar ganin takardun karatun Tinubu

0
633

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata kotu a Amurka ta umurci Jami’ar Jihar Chicago da ta bai wa Atiku Abubakar damar ganin takardun karatun Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Alƙaliyar kotun, Nancy Maldonado, ta yi watsi da buƙatar Tinubu na ƙin amincewa Atiku ya ga takardun, inda ta ba da wa’adin kwanaki biyu ga Jami’ar don miƙa wa Atiku takardun.

Ta kuma amince da hukuncin da alƙalin wata kotun majistre a Amurka, Jeffery Gilbert ya yanke a ranar 20 ga Satumba, wanda ya umarci Jami’ar ta Chicago da ta saki takardun karatun Tinubu kamar yadda Atiku ya buƙata, inda ta jaddada cewa Atiku yana da damar samun takardun.

A cewar alƙaliyar, dole ne Jami’ar ta kammala duk wani abu da ya kamata don sake takardun nan da ranar Talata.

Idan za a iya tunawa, ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakara, ya garzaya wata kotu a Amurka domin ta tilasta wa jami’ar Chicago ta saki takardun karatun Tinubu, domin hakan zai ba shi damar ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Febrairu.

Ɗan takarar na PDP ya buƙaci samun takardun ne don amfani da su a kotunan Najeriya wajen tabbatar da hujjarsa cewa takardun Tinubu na jabu ne.

Leave a Reply