Jam’iyar NNPP ta amince da korar Kwankwaso daga jam’iyar

0
175

Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta amince da rushe kwamitin ayyuka na (NWC) ƙarƙashin jagorancin Abba Kawu Ali. Legit Hausa ya wallafa.

Kwamitin BoT ta kuma tabbatar da korar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, rahoton Nigerian Tribune.

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a ƙarshen taron BoT na jam’iyyar NNPP wanda ya gudana a Otal ɗin Rockview da ke Apapa, jihar Lagas a ranar Juma’a, 28 ga watan Satumba.

KU KUMA KARANTA: Kwankwaso zai canza tambarin jam’iyar NNPP

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar na 2022 zai ci gaba da kasance yadda yake cewa ba za a yi la’akari da gyara shi ba har sai bayan babban zaɓen 2027.

Sakataren labaran jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Abdulsalam Abdulrasaq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka gabatarwa manema labarai.

Leave a Reply