Kagame zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a Rwanda

0
338

Shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame ya ce zai sake tsayawa takara a shekara mai zuwa, yana mai fatan tsawaita mulki kusan kwata na karni.

Mista Kagame, wanda ya zama shugaban ƙasa a shekara ta 2000, yana da damar ci gaba da mulki har na tsawon shekaru goma bayan da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima a shekara ta 2015, wanda ya sauya wa’adi da zai tilasta masa sauƙa daga mulki bayan shekaru biyu.

An tambaye shi a wata hira da mujallar Jeune Afrique ta Afirka ta Kudu da aka buga ranar Talata game da aniyarsa ta zaɓen baɗi.

“Na yi farin ciki da ƙwarin gwiwar da ‘yan Rwanda suka nuna a gare ni. Kullum zan yi musu hidima, gwargwadon iyawa. Eh, haƙiƙa ni ɗan takara ne,” inji shi.

KU KUMA KARANTA: DSS tayi gargaɗi ga ‘yan siyasar da ke shirin yin zanga zanga a ofishinta

Mista Kagame ya lashe zaɓen da ya gabata a watan Agustan 2017 na wa’adin shekaru bakwai da kashi 98.63% na ƙuri’un da aka kaɗa, a cewar hukumar zaɓen.

Shugaban ya samu karɓuwa a duniya wajen jagorancin zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙi tun bayan kawo ƙarshen kisan kiyashin da aka yi a shekarar 1994, inda aka yi ƙiyasin kashe ‘yan ƙabilar Tutsi da ‘yan ƙabilar Hutu masu matsakaicin ra’ayi sama da 800,000.

Sai dai ya fuskanci suka mai tsanani kan abin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka ce na murƙushe ‘yan adawar siyasa da murƙushe kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.

Mista Kagame ya yi watsi da waɗannan zarge-zargen. A shekarar 2015 Amurka ta soki sauyin kundin tsarin mulkin ƙasar, tana mai cewa kamata ya yi Mista Kagame ya sauƙa daga mulki idan wa’adinsa ya kare, kuma ya ba da dama ga sabbin shugabanni su zo.

A cikin hirar da aka yi da Jeune Afrique, Kagame ya ce bai damu da sukar da ƙasashen yammacin duniya ke yi masa ba.

“Ya kamata mutane su kasance masu zaman kansu kuma a bar su su tsara kansu yadda suke so,” in ji shi.

Leave a Reply