Ma’aikatar lafiya a jihar Neja, ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu a jihar

Ma’aikatar lafiya ta jihar Neja ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu guda biyar saboda rashin cancantar ma’aikata da kuma rashin sabunta rajistar wuraren aikinsu na shekara ta 2023.

Cibiyoyi biyar da abin ya shafa sun haɗa da Prince Clinic a Tunga, Union Diagnostic a Minna, Triple Medical Diagnostic a Bosso, Chall Dental a Minna, da Daza Primary Healthcare a Beji.

An rufe asibitocin ne a lokacin wani binciken bazata ga cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu guda 40 a ƙananan hukumomin Bosso da Chanchanga da sashen sa ido na ma’aikatar lafiya ta gudanar.

Mataimakin shugaban sashin kula da lafiya wanda kuma shi ne mataimakin darakta a sashen kula da lafiya da horaswa, Usman Abubakar Bosso ya bayyana cewa asibitin da abin ya shafa ba su yi rajista da ma’aikatar lafiya ba kuma ma’aikatar ba ta da bayanansu.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Zulum ya kai ziyarar bazata a asibitin Gwoza, ya yi takaicin ganin asibitin

Ya kuma ce an gargaɗi wasu asibitocin da dama kan rashin tsaftar muhalli a lokacin atisayen.

Bosso ya ce: “Wannan ya nuna cewa muna da ayyuka da yawa da aka rage mana.  Galibin waɗannan asibitocin hatsari ne ga rayuwar marasa lafiya.  Daga yanzu, za mu fara irin wannan ziyarce-ziyarcen bazata a wurare masu zaman kansu don ɗaukaka matsayin kiwon lafiya.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *