Mutane 33 da aka sace a Bauchi, sun kuɓuta

0
237

Sama da mutane 33 da aka yi garkuwa da su da suka haɗa da mata da ƙananan yara sun sami ‘yanci sa’o’i 24 bayan an yi garkuwa da su da bindiga a ƙaramar hukumar Alƙaleri ta jihar Bauchi.

An ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su ne biyo bayan umarnin da gwamnan jihar Bala Mohammed Abdulƙadir wanda ya fito daga yankin ya bayar.

An samu labarin cewa rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta haɗa kai da ‘yan ta’addan tare da samun nasarar kuɓutar da dukkan mutanen 33 da aka yi garkuwa da su.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Alƙaleri, Kwamared Bala Ibrahim Mahmoud ya karɓi baƙuncin waɗanda abin ya shafa a daren Juma’a daga jami’an tsaro a Yalwan Duguri a ƙaramar hukumar Alƙaleri.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun ƙubutar da mutane 25 daga Boko Haram

Mahmoud ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da mutanen a kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwa suka shiga dajin.

Mahmoud ya yaba wa jami’an tsaro bisa gaggauwa da matakin da suka ɗauka wanda a ƙarshe ya kai ga sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ya yi alƙawarin cewa dukkan mutanen 33 da aka sako da aka sace za a duba lafiyarsu kafin wani mataki na gaba.

Ƙaramar hukumar Alƙaleri dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin uku a jihar Bauchi da ‘yan fashi da makami ke yin ranar fage, suna garkuwa da mutane yadda suka ga dama tare da karɓar maƙudan kuɗaɗen daga iyalan waɗanda abin ya shafa.

Leave a Reply