‘Yan bindiga sun kashe mutane huɗu, sun sace 18 a Sakkwato

Rundunar ‘yan sanda a jihar Sakkwato ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Giyawa da ke ƙaramar hukumar Goronyo a yankin ‘yan majalisar dattawa ta gabas a jihar, inda aka tabbatar da mutuwar mutane huɗu.

Wata majiya a ƙauyen ta shaida wa wannan jarida cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki garin ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a kan babura da dama.

Majiyar ta ce “Sun mamaye ƙauyen mu jim kaɗan kafin Sallar Subhi (Sallar Asubah) a kan babura kuma suka fara harbe-harbe a gidaje da kuma mutanen da ke shirin koma wa gida daga masallaci.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe fastoci 23, sun rufe coci sama da 200 a Kaduna – Ƙungiyar CAN

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, Ahmed Rufa’i, ya tabbatar wa da ‘yan jaridan Najeriya cewa maharan sun sace mutane goma sha takwas da farko waɗanda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja da suka haɗa da dabbobi.

Ya ce daga baya bakwai daga cikin waɗanda aka sace sun tsere sun koma unguwarsu inda mazauna yankin da dama suka gudu domin tsira.

Ko da yake wasu majiyoyi daga al’ummar da abin ya shafa sun ce an sace sama da mutane 30, ‘yan sanda sun ci gaba da cewa mutum goma sha ɗaya ne kawai ke tare da maharan.

Rundunar ‘yan sandan ta ce jami’anta na bin maharan kuma suna ƙoƙarin ganin an dawo da zaman lafiya a cikin al’umma da muhallin da abin ya shafa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *