An kama mutane shida da ake zargi da kisan DPO na Ribas

0
235

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da kashe DPO na jihar Rivers, SP Baƙo Angbashim.

A baya dai LIB ta ruwaito cewa an kashe Baƙo ne a yankin Odiemudie da ke ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas (LGA) a jihar a yayin wani artabu da wasu ‘yan ƙungiyar asiri a yankin.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko ya fitar, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Ribas, CP Nwonyi Emeka Polycarp, tare da tawagarsa sun gudanar da wani samame a ranar Asabar 9 ga Satumba, 2023, da misalin ƙarfe 06:00 na safe a unguwar Odumude dake ƙaramar hukumar Ahaoda ta gabas ta jihar Ribas da nufin ƙwato gawar DPO da ya rasu tare da gudanar da aikin tantance al’ummar yankin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Bindiga Sun Kashe DPO Na Jibiya Da Soja A Jihar Katsina’

Ta ce a yayin wannan samame, an kama mutane shida da ake zargi a cikin al’umma.  Daga cikin kayayyakin da aka kama har da wata bindiga ƙirar gida da kuma layu iri-iri. 

Waɗannan waɗanda ake zargin da kuma kayayyakin da aka ƙwace a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda kuma suna fuskantar tambayoyi a CID na Jihar a birnin Fatakwal. Tun bayan faruwar lamarin, al’ummar yankin sun tsere saboda fargaba.

Bugu da ƙari, an sanya sabon DPO, SP Zuokumor Richard, zuwa sashin.  Yana tare da rabin dakaru daga Mopol 48, kashi ɗaya bisa uku na Mopol 19, askarawa 56, daga ƙungiyoyin dabaru. 

An ɗora masa alhakin gudanar da bincike mai zurfi a yankin, da kamo waɗanda suka yi sanadin mutuwar DPO, da ƙwato gawarsa, da kuma gano makami da aka yi amfani da su. 

Za a ci gaba da gudanar da wannan aiki yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply