EFCC ta mayar wa wata mata miliyan 19 da gida da mota

2
244

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta miƙa kadarorin da ta ƙwato daga hannun wani ɗan damfara mai suna Aisosa Ohue, wanda aka fi sani da Frederick Leonard, ga wata Ba’amurke da aka kashe, Cheryldene Cook.

Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, kadarorin sun haɗa da zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 19 da kuma wani gida mai ɗaki uku da ke Ward 36A Amagba a ƙaramar hukumar Oredo ta Edo. Ya ce, kadarorin da suka haɗa da Lexus E350 saloon mota, iPhone 13 Pro Max da kuma wayar Samsung A31, kwamandan shiyyar, ACE I Adebayo Adeniyi da shugaban sashin zamba na 1 ne suka miƙa wa matar a Abuja, ACE II Jimoh Rauf.

Uwujaren ya ce Cheryldene Cook da ta taso daga ƙasar Amurka domin karɓar kayayyakin ta samu rakiyar lauyanta, Dakta Mike Nwosu a gaban hukumar.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama mutane 23 da ake zargi da damfara ta yanar gizo

Ya ƙara da cewa ta miƙa godiyar ta ga hukumar bisa samun sauƙi.

A cewarsa, Mai shari’a C.E Nwecheonwu na babban birnin tarayya, Kuje ya bayar da umarnin a ƙwace kadarorin a watan Janairu bayan da aka samu Orhue da tuhume-tuhume uku da suka haɗa da samun kuɗi ta hanyar ƙarya.

“Wanda aka yanke wa hukuncin ya yaudari wanda aka zalunta ne ta hanyar zamba ta soyayya yayin da yake nuna cewa shi shahararren ɗan wasan kwaikwayo ne, Frederick Leonard”.

2 COMMENTS

Leave a Reply