Mun bar wa Bazoum wayarsa a hanunsa – Shugaban Sojin Nijar, a tattaunawarsa da Malaman addini (Bidiyo)

0
209

A makon da ya gabata ne, tawagar Malaman addini daga Najeriya, karkashin Shaikh Abdullahi Bala Lau suka isa jamhuriyar Nijar don tattaunawa da shugaban Sojin Nijar, Abdurrahman Tchiani. Bayan sun tattauna sun dawo, sashen Hausa na Muryar Amurka ta tattauna da Shaikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi, inda ya bayyana yadda suka tattauna kamar haka;

“Shugaban mulkin Soji na Nijar ɗin ya ce, na gaya wa yara na, ba na son ko jinin mutum ɗaya ya zuba a lokacin wannan juyin mulkin. Kuma ko Kaza ba a kashe ba. Juyin mulki ne na cikin gida.

Ya ce, abu ne zai faru suka hango, wanda idan ya faru, zai shigo har Najeriya, saboda shi ne sai suka yi ƙoƙari suka kare. Ya ce, ba su zo don su zauna ba. Su Sojoji ne, sun zo ne kawai a yi gyare-gyaren da za’a yi, su mayarwa ‘yan siyasa abinsu.

Amma su abin da yake ba su baƙin ciki har yanzu shi ne, da ba a ƙira su, an ji dalilansu ba. Sai kawai aka ɗora musu takunkumi. Sannan ya ce an yanke musu wutar lantarki, kuma abinci ba ya shigo wa. Wutar lantarkin nan kowa ya sani yarjejeniya ce tsakanin Najeriya da Nijer.

Lallai ya nuna suna neman alfarma a mayar musu da wuta. Sannan akwai waɗansu maganganun, waɗanda Insha Allah sai an je an ga shugaban Najeriya”.

Tambaya: Ko kun samu kun ga tsohon shugaban ƙasar Nijar ɗin Bazoum, wanda ke tsare?

KU KUMA KARANTA: Rufe iyakar Nageriya da Nijar ya sa mun tafka asara – ‘Yan kasuwar Sakkwato

“Mu ba mu nemi ganinsa ba, saboda a cikin maganarsa (shugaban mulkin Soji na Nijar) ya kawo maganganun da wataƙila ba sai mun tambaye shi ba. Kafin mu tafi an ce lallai idan an je za’a nemi ganin shi.

Amma mun masa tambayoyi. Kamar na cewa shugaba Bazoum ɗin yana cikin wahala? Sai ya ce, Bazoum ba ya cikin wahala, saboda mun bar shi da wayarsa a hanunsa har yanzu, kuma yana ƙiran waya. Duk waɗanda yake magana dasu muna ji.

Sai Shaikh Bala Lau ya tambaye shi cewa, an ce iyalansa ba kwa ba su abinci?
A’a muna ba su abinci, kuma sai mun tabbatar da lafiyar abincin ake ba su. Sannan batun rashin lafiyarsa, akwai likitansa kullum sai ya zo ya duba shi. Ko jiya ma sai sa ya zo ya duba shi”.

Kalli bidiyon a nan:

Leave a Reply