Hukumar ‘yan Sanda sun gargaɗi NLC kan zanga-zangar da suka shirya yi

2
365

Muƙaddashin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya bayyana damuwa kan zanga-zangar da ƙungiyoyin ƙwadago suka shirya yi, inda ya yi gargaɗin cewa ‘yan sanda ba za su lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba.

KU KUMA KARANTA: Jirgin sama mai sauƙar ungulu ya faɗo a Legas

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce ‘yan ƙasa suna da ‘yancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya yi tanadi amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ‘yan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zanga tana rikiɗewa ta zama tashin hankali, saboda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.
ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun shirya fara zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da soke tallafin mai da gwamnati ta yi.

2 COMMENTS

Leave a Reply