‘Yan Najeriya a ƙara haƙuri, daɗi nan tafe – Tinubu

2
352

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙira ga al’umma, musamman matasan ƙasar da su ƙara haƙuri kan halin matsin rayuwa da suke fuskanta a yanzu.

Tinubu ya bayar da tabbacin cewa wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a yanzu za su zamo daɗi a nan gaba.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin matasa na jam’iyar APC daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ya shaida wa matasan cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da matasa a dukkan matakan da za ta riƙa ɗauka, ya kuma ƙara da cewa “ba zai yi shakkun ɗaukar kowane mataki da zai kawo ci gaba da haɗin kan ƙasa ba.”

KU KUMA KARANTA: Masu sayar da man fetur na arewa sun yi barazanar shiga yajin aiki

Shugaba Tinubu ya ce ya fahimci irin raɗaɗin da ‘yan ƙasar ke ciki “Na yi rantsuwa ga ƙasata cewa ba zan yi shakkar ɗaukar kowane irin matakin da zai samar da ci gaba da tabbatar da haɗin kan ƙasar nan ba.

“Matakan farfaɗo da tattalin arziƙi kan ɗauki lokaci kafin a fara ganin alfanunsu. Ku ƙara haƙuri kaɗan.”

2 COMMENTS

Leave a Reply