Mashaƙo: Gwamnatin Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane biyu

0
361

Hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Bauchi, (BSPHCDA), ta tabbatar da ɓullar cutar mashaƙo (diphtheria) a ƙananan hukumomi shida na jihar.

Shugaban hukumar Dakta Rilwanu Mohammed ya tabbatar da ɓullar cutar a wani taron manema labarai ranar Laraba a Bauchi.

Ya ce hukumar ta tattara samfurori 58 na waɗanda ake zargin sun kamu da cutar daga watan Janairun 2023 zuwa yau.

KU KUMA KARANTA: Sanata Bomoi ya ba da gudumawar naira miliyan ɗaya ga asibitin ƙwararru na Potiskum don daƙile cutar mashaƙo

“Biyu daga cikin ukun da aka tabbatar sun kamu da cutar diphtheria sun mutu a ƙaramar hukumar Jama’are ta jihar.

“Waɗannan cutar galibi suna tsakanin wanda suke kiwo ne da kuma yaran da ba a musu allurar rigakafi.

“Cutar tana tsakanin yaran da ke tsakanin watanni takwas zuwa shekaru huɗu, kuma akwai wani yaro ɗan shekara bakwai.

“Hukumar ta rufe makarantu a Jama’are saboda rahoton da ake zargin sun kamu da cutar a wata makaranta,” inji shi.

A cewar Mohammed, hukumar za ta ƙara yawan allurar rigakafin da ake yi wa ɗaliban a makarantu a faɗin yankunan da abin ya shafa.

A halin da ake ciki, hukumar ta tabbatar da ɓullar cutar zazzabin bayan rahoton mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar a ƙananan hukumomin Dambam, Ganjuwa da Jama’are.

“Muna da wasu ƙararraki guda tara masu inganci waɗanda biyar aka tabbatar da su,” kuma sun yi watsi da jinkirin da ke haɗe da samun sakamakon waɗanda ake zargi daga ɗakin gwaje-gwaje.

“Ana aika samfurori daga jihohin zuwa ɗakin gwaje-gwaje na ‘National Reference Laboratory’ da ke Abuja inda ake kai su Dakar a Senegal, wannan ita ce matsalar da muke fuskanta.”

Leave a Reply