‘Yan bindiga a jihar Anambara sun sace wani boka

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani shahararren boka ɗan asalin jihar Anambara, mai suna Chinedu Nwangwu a ɗaya daga cikin otel ɗin sa a ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa.

Bokan da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki, na nufin ‘ƙwai mai karya ƙwaran manja’ a turance.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mataimakansa guda biyu a lokacin da aka yi garkuwa da shi a daren Lahadi.

Wata majiya ta ce mutumin wanda ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya ƙarfi a jihar ta Anambara, an yi garkuwa da shi cikin sauƙi a otal ɗin sa mai suna Triple P Hotel, tare da bindige wasu muƙarraban sa guda biyu har lahira.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

Ana kuma kallon Akwa Okuko Tiwaraki a matsayin mai maganin gargajiya mafi kuɗi a jihar.

A 2022 ya gina tare da ƙaddamar da otal guda biyu, waɗanda aka ɗauka a matsayin mafi girma a Oba.

Majiyoyi, sun ce sace shi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya ƙarfi.

Hukumomin ‘yan sanda a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda ma magana da yawunsu, DSP Toochukwu Ikenga ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, sai dai daga bisani an sako bokan da aka sace.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *