‘Yan bindiga sun sace matafiya a Edo

0
243

Wasu gungun ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, waɗanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun yi garkuwa da wasu fasinjoji da ba a bayyana adadinsu ba a hanyar Jesse-Oben, wanda ke kan iyaka tsakanin jihohin Edo da Delta.

Lamarin ya faru ne a kusa da Oben, al’ummar da ta shahara wajen samar da mai da iskar gas a jihar Edo.

A cewar shaidun gani da ido, waɗanda lamarin ya rutsa da su na tafiya ne daga Sapele da ke jihar Delta a lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa motar su kwanton ɓauna.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun ce sun ceto mutum 40 daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara

Nan take masu garkuwa da mutanen suka fito daga daji suna harbin iska, inda suka tilasta wa direban ya tsaya.

Ɗaya daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da ita ‘yar wani mai sayar da jaridu ce mai shekaru 24 da haihuwa.

Sai dai abin takaicin shi ne direban da kwandastan sun yi nasarar tserewa yayin da masu garkuwar suka nufi sauran fasinjojin zuwa cikin daji.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Child Nwabuzor, domin jin ta bakinsa, ya bayyana cewa bai san da faruwar lamarin ba amma ya tabbatar da cewa zai ci gaba da bincike kan lamarin.

Leave a Reply